Wasu daga jami'an sojoji da aka tura yankin Abule dake garin Ikorodu a jihar Lagos sun gamu da ajalinsu a sanyin safiyar jiya Juma'a a yayin wani artabu da suka yi da wasu barayin mai.
Wata majiya daga rundunar tsaro ta tabbatar mana da cewa barayin wadanda suka iso kusan su dari, sun budewa sojojin wuta a yayin da suke kan farauta a yankin na Abule, inda suka kashe biyar daga sojojin a yayin bata-kashin da aka kai kusan awa guda ana fafatawa.
Majiyar ta kara da cewa an ga uku daga cikin gawar sojojin ruwan tare da makamansu a jikinsu, inda kuma har zuwa yanzu ba a gano inda ragowar biyun suke ba.
Majiyar ta kuma kara da cewa, a ranar Larabar da ta gabata, barayin man sun kai wa sojojin farmaki, amma ba su yi nasara ba, inda sojojin suka fatattake su.
Title :
Barayin Mai Sun Kashe Sojoji Biyar A Jihar Lagos
Description : Wasu daga jami'an sojoji da aka tura yankin Abule dake garin Ikorodu a jihar Lagos sun gamu da ajalinsu a sanyin safiyar jiya Juma'...
Rating :
5