Dattijo mai kare hakkin dan Adam, Dakta Tunji Braithwaite, ya bayyana cewa tsoffin shugabannin kasa, Olusegun Obasanjo da Janar Ibrahim Babangida, su suka cusawa gwamnonin kasar nan ra'ayin cin hanci da rashawa.
Braithwaite ya ce salon mulkin tsoffin shugabannin shi ya sanyawa gwamnonin sha'awar cin hanci da rashawa, inda ya kara da cewa da yawa daga cikin gwamnonin suna koyi ne da su Babangida da Obasanjo a bangaren cin hanci da rashawa.
Mai rajin kare hakkin dan Adam din, ya bayyana hakan ne a yayin hirar da ya yi da jaridar Punch a jiya Talata.
Sannan kuma ya bayyana hakan ne biyo bayan furucin da Obasanjo ya yi na cewa gwamnoni suna gudanar da rayuwa mai tsada amma al'ummarsu na cikin kuncin rayuwa.
Title :
Babangida Da Obasanjo Ne Suka Cusawa Gwamnoni Sha'awar Cin Hanci Da Rashawa - Dr Tunji
Description : Dattijo mai kare hakkin dan Adam, Dakta Tunji Braithwaite, ya bayyana cewa tsoffin shugabannin kasa, Olusegun Obasanjo da Janar Ibrahim Bab...
Rating :
5