Sanda mukayi tafiyan kusan awa4 kafin nan suka tsaya suka bude kofan manyan mata 5 da yara 2suka iba daga ciki ko harda maman wannan yarinya dan allah ku tsaya na dauki yar ta amma basu saurare taba dan allah baiwar allah ga amana yar ta ke ta sani ki rike min amananta dan allah jan matan suke har suka shige da ita cikin bayan awa guda sai gasu sun fito suka rufe kofan motan kallon yarinyan da baza ta wuce shekara 6 ba wace yunwa yasa ta baccin dole allah sarki ynxu bake ba mamanki tausayin muh ni da itane ya kamani tsayuwan motan naji na tabbatar da mun iso bude kofan sukayi a daidai lokacin wannan yarinyan ta tashi kiran mamanta ta fara yi tausayinta ne ya kamani na dauki ta ina rarashin ta na fara tare da daukan ta haka tako yi shiru sai ajiyan zuciya take mutanan suka ce muh shiga cikin katon gidane wanda ko ba a fada mah ba kasan gidan sarautane nan .
.
Fadawan da suke tsare bakin gate din suh suka tambaya gun wah mukazo wanda suka kawo sukace bayi muka kawo zare ido nayi kenan ni yau fateema ce xan xama baiwa Alahalin ni BA BAIWA BACE hawaye suka fara xuba a ido na fada wan sukace muh tsaya anan bari a kira jakadiyan ko wace gimbiya ba suh jimaba suka dawo da wasu mata guda 2 matan ne suka raba muh ko wace ta tadauki2 amma aka bar min mufeeda dan acewar matan mufeeda yar tace wani side aka shiga palo muka shiga ya tsaru iya tsaruwa duk abinda ake nema a gidan sarauta akwoi a cikin matar da ta shigo damu tace mana muh tsaya bari taje ta samu gimbiya ta sanar mata da zuwan mu. Wani kofa da mukaga ta shiga bata jima ba ta fito ta ceh mana muh biyo ta kofan da mukaga ta shiga nan muka shiga bayi muka gani sunata hidimomin su labule ta daga tare da neman ixini dan ta shigo wata mata muka gani wace baxa ta wuce shekara57 ba tana kishingede akan gado tare da kayan friut a gaban ta bayi sai hidima suke mata wannan matan ne ta suguna tare da yin kirari muma muka yi yarda wannan matan tayi ran ki ya dade ga bayin an kawo maki daga ido tayi tare da kallon muh a walakance wannan ni ta nuna tare da tmby meye sunana Fateema ran ki ya dade tsawa ta dakamin wanda sanda Mufeeda ta fara kuka ke har kin kai ana ce maki fateema kina baiwa jakadiya gara ku san yarda xa kuyi dan baxan kirata da fateema ba dan sunan yarinya tace . Ran gimbiya ya huce tare da yi mata kirari irin nasu na sarakuna murmushi gimbiya tayi wanda zai nuna mah alaman ta huce ke baiwa daga yau sunan ki ya tashi daga fateema zuwa Batula ina fatan kin gane hawaye ne ya ciko min ido fateema xarah Abba na ya samun ran sunnan amma gashi yau an canja min mgn jakadiya naji shiya dawo dani daga tunani da nake naji ran ki ya dade jakadiya wannan aikin ta xatana gyara wasu yarana side dinsu da kuma kula dasu dan naga aikin daza ta iya kenan angama ranki ya dade ki baiwa tashi muje wannan matan kuma a sata a wajen yan hidimomin cikin gida angama gimbiya tareda hada mata kirari.
.
Wani daki jakadiya take ni tare da bani wasu kaya kala 3 ta umurceni dana canja na jikina ke Batula idan kin canja ki same ni a waje dan na nuna maki aiki da zakinayi to kawea na ce mata tareda canjawa na fito wani bangare muka nufa kafin muh karasa muka fara jin hayaniya kida salama jakadiya tayi wanda basu saurare muh ba muka shiga wasu yam mata ne guda 3 wanda bazasu wuce shekaru 18-19 ba jakadiya da suka gani shiyasa suka kashe tare da juyawa. Kirari ta fara masu wanda shi ya kara sa suh ji da kansu hanu daya daga cikinsu ta daga wah jakadiya hanu alaman tayi shiru jakadiya me ya kawo ki tareda wannan baiwar ran gimbiya fateema ya dade gimbiyace ta ce akawo maku baiwa dazatana kulada ku,awulakance suke kallona wace aka kira da gimbiya fateema ce ta fara magana ok xaki iya xuwa kinunah mata abinda xata fara batayi shiru ba wace take kusa da ita jakadiya ta fara xuwa dakina ta gyara min to ran gimbiya Amira ya dade.wato sunan yaran fateema da amira sai ta karshen wace bata ceh komai ba,wani daki muka shiga dakin komai blue gashi ya sha kayan sarauta fita jakadiya tayi ta tareda tace komai ba dakina na gidan muh na tuna tareda tuna mamana, hassan da kuma dan baby muh kuka nayi mai isata kafin na shiga bayi na wanke bayan na gama na gyara dakin kafin na fito na samesuh kaman yarda na barsu. Na same kamar yarda na barsu durkusawa nayi kaman yarda naga jakadiya tanayi ran ki ya dade na gama shiru sukamin sanda gimbiya fateema ta ya musah fuska kafin nan tace ke ki tashi ki kawo mana abinci ko baki san lokaci yayi,mikewa nayi na bi kofan danaga jakadiya tabi na fito na hadu da jakadiya ke baiwa Batula kixo ki kai wasu gimbiya abinci to binta nayi ta nunah min yarda xan yi komai na kaimasu har ynxu wannan ta ukun suh bata yi magana ba komai naga da kanta take yin sa.
.
Ayau na cika wata 2 a fada ba tare da nasan wannan wani gari bane balle har nasan sunnan masarautan .ina daki ina bawa mufida abinci naji ana kirana kuma ba gimbiya fateema ko gimbiya Amira sallama naji wanda duk cikin suh ba wace ta taba min sa bude kofan da akayi ne ya dawo dani daga tunani dana yi gimbiya ta ukuce wace har yau bansan sunnan ta ba murmushi tamin wanda sai ynxu naga kyau ta kuma duk cikin suh ita ka daice fara sol kuma mai gashi cikin suh.Gaisuwa na fara yi mata wanda murmushi kawea tamin tare da daga min hanu alamun yayi hanun mufida naga ta kama tare da daura ta akan cinyarta kallon ta na fara yi cikin mamaki rae ki ya dade baiwa ce ita bai kamata ta hau cinyar ki ba gimbiya kara jawo mufida tayi jikin ta dama ga mufida da san jiki tinnin ta fara vacci. 18 Batula ina ji a jikina cewa ke BA BAIWA BA shiyasa tin randa jakadiya ta kawo ki ran ki ya dade ni da yar nan bayi ne da gaske ynxu dai first of all wat ur real name sunana fateema amma randa aka kawo ni jakadiya ta canja mim xuwa Batula murmushi naga tayi ajiyan zuciya naga tayi kinga ynxu na kamaki na tmby ki da turanci kuma kin ban amsa shin baki yarda dani bane fati ran ki ya dade ba haka bane ina jin tsoro ne shiyasa ki yarda dani kinji lokaci daya naji na yarda da ita a lokaci na bata labari kai na hawayene nagani a idon ta a lokaci daya na kidime.
.
Mu Hadu Anjima Da Rana Don Jin Karikon Labarin.
#Hausa Novel 📓
#IPh
Title :
Ba Baiwa Bace Part 2
Description : Sanda mukayi tafiyan kusan awa4 kafin nan suka tsaya suka bude kofan manyan mata 5 da yara 2suka iba daga ciki ko harda maman wannan yarin...
Rating :
5