sauda dama idan muna rubutu akan illolin auren dole wasu iyayen gani sukeyi kamar ana koyawa yan mata mummunar dabi a donsu bijerewa iyayenesu suki bin umarnin iyaye
yanada kyau mugane Yiwa yan mata auren dole,
wata al'adace da muka
dade a cikin ta, kuma ta
haifar da matsaloli, masu
yawa, wasu mata sun shiga
karuwanci saboda auren
dole, wasu sun kashe
kansu saboda auren dole,
wasu sun kashe mazan
saboda auren dole, wasu
sun sami nakasa, saboda
auren dole, wasu sun
zauna cikin damuwa da
bacin rai, da bakin ciki,
saboda auren dole, wasu
sun kashe yayan da suka
haifa saboda basason
auren, kin da suke wa uban
ya shafi yayan.auren dole yana saka mace hana miji hakkinsa na aure babu shakka auren dole yasaka mata da dama sabon allah
Na taba yi muku misali da lokacin Manzon Allah (saw) anyi wani
mutun da ake kira da suna Mughir
wanda Allah ya jarrabe shi da
tsananin son wata mata da ake kira
da suna Barira, amma kuma cikin
ikon Allah ita kuma duk duniya
babu wanda bataso irinsa
(Mugheer), har saida takai yana bin ta a hanya, yana kuka, yana
rokonta, da ta soshi, amma ita
kuma ta kekasa kasa. Wata rana
sahabbai suka ga irin halin da
mughir ke ciki, suka cewa manzon
Allah shin baza kashiga cikin
al’amarin Mughir da Barira ba,
Manzon Allah Salallahu Alaihi
Wasallam, da kansa yace hakika
anjarrabi Mughir da soyayyar
Barira. Manzon Allah ya taka da
kafarsa mai daraja, yaje wajen
Barira da kansa Salallahu Alaihi
Wasallam, ya ce yanzu Barira baza
kiso Mughir ba! Ta ce ya Manzon
Allah! kana bani umarni ne, ko
kuma kana bani shawara, yace ina
baki shawara ne salallahu Alaihi
Wasallam, ta ce ya Manzon Allah
bana sonsa, haka Manzon Allah ya
taso yana mamakin irin yadda
zuciyar Barira bata nutsu da Mughir ba duk kuwa da irin yadda yake nuna soyayya a gareta.
to anan da auren dole yana da
muhalli a musulunci da Manzon
Allah ya umarci Barira ta auri
Mughir sai dai baiyi hakan ba.
Wannan shi ya nuna mana cewa
addinin Musulunci bai yarda da
auren dole ba, domin da ana yi, da saboda yadda Manzon Allah ya tausayawa Mughir da ya umarce ta da ta aureshi amma haka ya bata cikakken ‘yancin ta salallahu alaihi wasallam
to kunga yanada kyau iyaye su fahimci auren dole al adace ba wai addiniba
sannan suma kansu yan mata akwai nasu laifin domin yan mata da dama basa duba mutuminda ya dace su aura.
Title :
Auren Dole
Description : sauda dama idan muna rubutu akan illolin auren dole wasu iyayen gani sukeyi kamar ana koyawa yan mata mummunar dabi a donsu bijerewa iyayen...
Rating :
5