Wata kotu a kasar Misira “Egypt” ta yanke ma wani yaro dan shekaru 4 da haihuwa hukuncin daurin rai-da-rai a gidan kasu. Ana dai tuhumar wannan rayon ne da laifin kisa a lokacin da yake dan shekara daya da haihuwa. Cikin laifufukan da ake tuhumar yaron Ahmed Mansour Karmi, sun hada da kisa, yunkurin kisa har sau 8, lalata dukiya, da yin barazana ga sojoji da ‘yan-sanda, duk a lokacin da yake dan shekara daya da rabi da haihuwa.
Shi dai yaron Ahmed, an yanke mishi wannan hukuncin ne tare da wasu mutane 115, da aka yanke ma hukuncin daurin rai-da-rai a kotu da ke yankin yanma da kasar, a cikin zargin da ake na aikata laifin a shekarar 2014. Lauya mai kare yaron Faisal Al-Sayd, ya fadama manema labarai cewar, an saka sunan yaron ne bisa kuskure, amma kotun bata duba shekarun yaron ba da aka haifa a shekarar 2012, sai kawai ta zartar da wannan danyen hukuncin a kanshi.
Ya kara da cewar, sun gabatar da takardar shedar haihuwar yaron ga hukumar leken asisiri ta kasar, wanda daga nan sai aka maida karar kotun sojoji. Hakan dai na nuna cewar alkalin bai karanta kes din yaron ba, sai kawai ya yanke hukunci.
Wani lauya mai zaman kanshi yace, wannan kes din ya bayyanar ma duniya cewar, babu adalci a kasar Misira. Ya kara da cewar kasar na fuskantar mulkin mallaka a karkashin shugaban kasar Abdel Fatah Al-Sisi, tun bayan hanbarar da gwamnatin zababben shugaban kasar Muhammed Morsi, a shekarar 2013. Yanzu haka dai akwai ‘yan adawa sama da mutane 40,000 da aka kulle a gida kasu.
Source Dandalin VOA
Title :
Anyi Wa Yaro Dan Shekara Hudu Hukucin Rai Da Rai A Kasar Masar
Description : Wata kotu a kasar Misira “Egypt” ta yanke ma wani yaro dan shekaru 4 da haihuwa hukuncin daurin rai-da-rai a gidan kasu. Ana dai tuhumar wan...
Rating :
5