An Kama Wasu Mutane Biyu Akan Yaron Da Matsafa Suka Kwakwalewa Idanu A Garin Zaria
A yayin da rundunar 'yan sandan ta sanar da kama wasu mutane biyu bisa zarginsu da hannu a kwakwale idanun wani yaro dan shekaru uku a garin Zaria, yanzu haka ana shirin shillawa da yaron kasar Indiya domin ba shi kulawa. Mahaifin yaron mai suna Abubakar, wato Malam Usman Isa Auta, ya bayyanawa majiyarmu ta Daily Trust cewa, Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris shi ya dauki nauyin fita da yaron tare da daukar nauyin jinyarsa.
A watan da ya gabata ne wasu da ake zargin matsafa ne suka kwakwalewa Abubakar idanu a wani kango a unguwar Buda da ke yankin Jushi a garin Zaria. Tun daga wannan lokacin yaron yake kan karbar magani a asibitin koyarwa na jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria, inda daga bisani aka sallame shi.
Bincike ya nuna cewa likitocin na kokarin ganin an dasawa yaron idanun roba, domin maye gurbin idanun da aka cire masa.
Haka kuma mahaifin yaron ya kara da cewa, fitaccen Malamin addinin Musuluncin nan, wanda yanzu yake zama a Madina, wato Sheik Isa Ali Pantami ya dauki nauyin karatun yaron ta fannin addini da zarar an gana jinyarsa.
A ranar 9 ga wannan watan ma, wasu mutane sun yi yunkurin cire idanun wani yaro mai suna Ibrahim Mannir, a unguwar Sabuwar Banzazzau dake yankin Zaria. Wasu ganau sun bayyana cewa har mutanen sun daure yaron, kafin daga bisani 'yan banga suka gano su. Saidai mutanen sun arce kafin jama'a su zo.
Bayan kwana uku da aukuwar hakan ne, 'yan bangan yankin suka kama wasu mutane biyu da ake zargin suna da hannu a kwakwale idanuwan Abubakar. An kama su ne a ranar Juma'ar da ta gabata.
Majiyarmu ta ce an kama daya daga cikin wadanda ake zargin ne da misalin karfe 1:15 harabar wata makarantar firamare dake unguwar Buda a yankin na Zaria, a daidai lokacin da ake shirin zuwa sallar Juma'a.
A yayin da ake tambayarsa ko me yake yi a cikin harabar makarantar a daidai wannan lokaci? Wanda ake zargin ya fadi cewa ya zo hira ne wurin budurwarsa, inda kuma bayan an ce ya nuna gidan su buduwar da ya zo hira wurinta, ya gagara fada.
Kwamandan hedikwatar rundunar 'yan sanda shiyyar Zaria, Muhammad D. Shehu ya tabbatar da kama mutane biyun, inda ya ce yanzu haka an garzaya da su sashen binciken manyan laifuka dake Kaduna.
Title :
Ana Zargin Mutane Biyu Da Kwakwalewa Wani Yaro Idanunsa
Description : An Kama Wasu Mutane Biyu Akan Yaron Da Matsafa Suka Kwakwalewa Idanu A Garin Zaria A yayin da rundunar 'yan sandan ta sanar da kama was...
Rating :
5