Wani yaro dan shekaru hudu wanda da ne ga dogarin tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo, mai suna Nasirudden da wasu matan aure guda uku sun fada hannun wasu masu garkuwa da mutane a jihar Kaduna wadanda kuma har zuwa yanzu ba a gano su ba.
Dogarin tsohon mataimakin shugaban kasar, Sajan Mahmood Mohammed ya bayyanawa majiyarmu ta LEADERSHIP a jiya kan yadda aka yi garkuwa da dan nasa a rukunin gidaje na Marafa a garin Kaduna.
Sajen Mahmood ya ce da farko masu garkuwar sun sace da har da 'yarsa mai shekaru shida kafin daga bisani suka ajiye yarinyar a daidai titin Sultan suka tafi da yaron kadai.
Ya ce lamarin ya auku ne a ranar 19 ga watan Janairu na wannan shekara, a yayin da yake bakin aiki da tsohon mataimakin shugaban kasa a Abuja.
Ya ce tun daga wannan lokacin daga shi har iyalansa babu wanda ya yi magana da masu garkuwar.
"A lolacin da suka kwashi yaran, sun baiwa ta macen naira dubu daya da nufin ta je ta sayo nama ta dawo, inda kafin ta dawo suka yi awon gaba da yaron. Kuma tun daga wannan lokacin babu tabbacin inda aka nufa da shi kuma ba su kira mu ba", inji Sajen Mahmood.
A gefe daya kuma an yi garkuwa da wasu matan aure guda uku a wani kauye da ake kira Dorayi a karamar hukumar Zaria a jihar Kaduna.
Wani mazaunin yankin ya bayyanawa majiyarmu cewa masu garkuwan wadanda sun kai su goma, sun shigo kauyen ne a ranar Lahadin da ta gabata inda suka yi awon gaba da matan.
Majiyar ta mu ta bayyana sunayen matan a matsayin Maimuna Abubakar, mai shekaru 25, Mairo Hussaini mai shekaeu 20, da Hauwa Ibrahim mai shekaru 20.
A yayin da majiyarmu ta tuntubi ofishin rundunar 'yan sandan jihar, kakakinta DSP Zubairu Abubakar ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce suna kan gudanar da bincike.
Title :
An Yi Garkuwa Da Yaron Dogarin Namadi Sambo Da Wasu Matan Aure Guda Uku A Jihar Kaduna
Description : Wani yaro dan shekaru hudu wanda da ne ga dogarin tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo, mai suna Nasirudden da wasu matan aure guda ...
Rating :
5