A ranar Talatar da ta gabata ne , wasu da ba a san ko su wanene ba suka yi garkuwa da kawun tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan mai suna Ignite Jonathan mai shekaru 72.
Idan ba a mance ba a ranar 28 ga Fabrairu, 2014, an yi garkuwa da kawun nasa, amma daga baya jami'an tsaro suka gano shi a wani kauye da ake kira Akipli a ranar 10 ga watan Maris, 2014.
Bincike ya nuna cewa an yi garkuwa da kawun tsohon shugaban kasar ne da misalin karfe goma na safiyar ranar Talatar, a garin Otueke da ke karamar hukumar Ogbia a jihar Bayelsa.
Title :
An Yi Garkuwa Da Kawun Jonathan
Description : A ranar Talatar da ta gabata ne , wasu da ba a san ko su wanene ba suka yi garkuwa da kawun tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan mai suna...
Rating :
5