Masarautar garin Dutse dake jihar Jigawa ta sauke Mustapha Lamido daga mukaminnsa na Santurakin Dutse da na Hakimin Bamaina. Mustapha da na ne ga tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido.
Shi dai Mustapha da dan uwansa Aminu tare da mahaifinsu, ana zargin su da wawushe bilyoyin kudade mallakar jihar Jigawa, inda har ta kai ga an maka su a kotu.
Wsikar da ke dauke da sanarwa tsigewar mai lamba; ECD/69/VOL III/1060, mai dauke da kwanan wata 31 ga Janairu, 2016, mai dauke da sa hannun sakataren masarautar Dutse, Yunusa Garba, ta bayyana cewa an tsige shi Mustaphan ne ba tare da bata lokaci ba.
Sakataren ya ce an soke Mustapha ne daga sarautar sakamakon zargin da ake yi masa shi da mahaifinsa na satar dukiya, wanda hakan ya sabawa dokar farar hula sashe na 04301 da 04412.
Title :
An Warware Rawanin Sarautar Dan Gidan Sule Lamido
Description : Masarautar garin Dutse dake jihar Jigawa ta sauke Mustapha Lamido daga mukaminnsa na Santurakin Dutse da na Hakimin Bamaina. Mustapha da na ...
Rating :
5