Jami'an JTF dake karamar hukumar Konduga a jihar Borno sun kama wani jigo na 'yan Boko Haram, mai suna Bashir, wanda yake magana a madadin Abubakar Shekau a hotunan bidiyo da 'yan ta'addan ke fitarwa. An kama shine a jiya Juma'a, kamar yadda majiyarmu ta News Punch ta rawaito.
Majiyar ta kara da cewa a binciken da aka yi wanda ake zargin, wanda ake yi masa lakabi da Saekin Yanka, ya bayyana cewa ya jima yana magana a madadin Shekau a hotunan bidiyo da dama da 'yan ta'addan suke fitarwa, sannan kuma ya kara da cewa shi yake da alhakin kashe mahaifiyarsa da kuma 'yan uwansa mata guda biyu da namiji daya.
Malam Shettima Bulama, wanda yana daya daga cikin membobin JTF din da suka kama Bashir, ya bayyana cewa sun kama shine a yayin da yake kokarin shiga cikin garin Konduga. Kuma an gano tabon harbin mashi da aka yi masa. Haka kuma ya bayyana cewa ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.
Shettima ya kara da cewa, Bashir yana kama da Abubakar Shekau ta fuska.
Saidai majiyar ta mu ba ta samu tabbaci daga rundunar tsaro ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto, inda Kakakin rundunar Kanal Sani Usman Kukasheka ya bayyana cewa labarin bai zo musu tukunna, amma da zarar labarin ya zo musu, za su sanar.
Title :
An Kama Mai Magana A Madadin Shekau
Description : Jami'an JTF dake karamar hukumar Konduga a jihar Borno sun kama wani jigo na 'yan Boko Haram, mai suna Bashir, wanda yake magana a m...
Rating :
5