Da Alamu An Gano Tabbataccen Wurin Da Aka Boye Daliban Chibok
Da alamau an gano tabbataccen inda aka boye daliban Chibok da aka sace, kamar yadda rundunar sojojin saman Nijeriya ta tabbatar a daren jiya
Daraktan yada labarai na rundunar, Kyaftin Ayodele Famuyiwa, ya bayyanawa gidan talabijin na Channels cewa sakamakon haka ne dakarun sojojin saman suka tsagaita kai farmaki a wannan sashe don gudun kada a illata 'yan matan.
Idan za a tuna, a kwanan nan dakarun sojojin saman sun kai farmaki cikin dajin Sambisa inda suka tarwatsa sansanin 'yan Boko Haram dim, amma kakakin sojojin ya kara da cewa inda suka kai farmakin bai shafi sashen da 'yan matan suke boye ba.
An sace yaran ne makarantar sakandiren su ta 'yan mata dake garin Chibok a jihar Borno kusan shekaru biyu da suka gabata.
Idan ba a mance ba dai a makon da ya gabata tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa ba lallai ba ne a sake ganin 'yan matan, inda ya kara da cewa duk wanda ya ce za a gano su, ya yi karya.
Title :
An Gano Tabbataccen Wurin Da Aka Boye Daliban Chibok
Description : Da Alamu An Gano Tabbataccen Wurin Da Aka Boye Daliban Chibok Da alamau an gano tabbataccen inda aka boye daliban Chibok da aka sace, kamar...
Rating :
5