Yunkurin da gwamnatin Buhari ke yi na ganin bayan kungiya ina da kisa ta Boko Haram ya samu chanje-chanje domin bayanai na cewa tuni gwamnati ta chanja Janar Burutai daga shugabanci "Operation Lafiya Dole" da ake yin shi a Borno, Yobe da Adamawa.
Rahotnni sun ce tuni an baiwa Manjo A Olonishakin shugabanci yaki da Boko Haram din wanda shine CDS ya kuma fara karbar aiki daga Burutai wanda shine COAS.
Majiyar ta gano cewa an samu wannan sauyi, ne domin hedikwatar tsaro ta zama ita ke jagorantar wannan yaki ganin cewa Boko Haram na yunkurin kunyata ikirarin gwamnati na ganin bayan Boko Haram.
Wasu sojoji dake cikin wannan aiki na LAFIYA DOLE sun nuna damuwarsu ganin yadda ake kokarin shigo da siyasa kan wannan aiki ganin iri nasarar da aka samu a karshen 2015.
Masharhanta da yawa na ganin cewa wannan dalili yasa ba a Burutai a Dolari da ragowar garuruwan da aka kai hari ba ganin yadda yake bayyana da wuri in an kai hari a wannan yaki don karfafa soja
Title :
An Dauke Burutai Daga Kwamandan Yaki Da Boko Haram
Description : Yunkurin da gwamnatin Buhari ke yi na ganin bayan kungiya ina da kisa ta Boko Haram ya samu chanje-chanje domin bayanai na cewa tuni gwamnat...
Rating :
5