Almajiranci Ba Musulunci Ba Ne, Talauci Ne Ke Haddasa Shi, Inji Sarkin Musulmi
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar III ya bayyana a ijiya Asabar cewa almajiranci ba shi da alaka da Musulunci, kawai matsala ce ta talauci da ya addabi wasu iyayen yaran.
Kamar yadda Sarkin ya ce, da yawa daga cikin iyayen yaran da suka gagara tura 'ya'yansu makarantar Boko su suke tura su yawon barace-barace, inda ya kara da cewa komai ba ne ke haddasa hakan illa talauci.
“Almajiranci ba shi da hurumi a addinin Musulunci, matsala ce kawai ta talauci da ya addabi wasu daga cikin iyayen yara", inji Sarkin Musulmi.
Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne a jihar Kaduna a jiya Asabar, a yayin taro kan ilmin yara da ya jagoranta.
Title :
Almajiranci Ba Musulunci Ba Ne, Talauci Ne Ke Haddasa Shi - Sarkin Musulmi
Description : Almajiranci Ba Musulunci Ba Ne, Talauci Ne Ke Haddasa Shi, Inji Sarkin Musulmi Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar III ya bayyan...
Rating :
5