Daga Sani Musa
Al'ummar keffi dake jihar Nassarawa sun koka dangane da matsalar ruwan sha dake suke fama da ita.
Wasu daga cikin mutanen da suka zanta da wakilinmu, sun ce yau kusan shekaru uku kenan matsalar ruwan sha ya addabi mutanen Keffi, kuma gwanatin jihar ta Nassarawa ta ki yin wani abu domin magance wannan matsalar, duk da yawan alkauran yin hakan da ta sha yi a baya.
Wani mai suna Abdullahi Musa dake zaune a unguwar Karofi, ya ce mutanen garin Keffi na shan wahalar gaske wajen samun ruwan sha, musamman talakawa wadanda ba su da karfin gina rijoyoyin burtsatsai, kuma gashi a kullum garin sai bunkasa yake yi.
Wakilinmu ya gano cewa matatar ruwa daya dake garin karami ne wanda aka gina ta kusan shekaru 40 da suka shude kuma ba a fadada ta ba.
Duk kokarin da wakilin mu ya yi na jin ta bakin shugaban karamar hukumar Keffi Alhaji Dikko Abdullahi, ya ci tura, saidai wata majiyar gwanati ta ce Gwanan jihar Alhaji umar Tanko Almakura ya sha alwashin kawo karshen wannan matsalar wadda ta ki ci ta ki cinyewa.
Wata mata mai sana'ar sayar da abinci a kusa da gidan mai na Total dake Keffi, wadda ta ce ba ta son a bayyana sunanta, ta ce sukan sayi jarka guda na ruwa mai lita 20 akan naira hamsin ku dari, a wasu lokutan ma ba a samun ruwan. Ta ce Gwanan ya sha cewa za a gyara bututan ruwan Keffi saboda wai sun tsufa tare da lalacewa, amma shuru ake ji kamar an shuka dafaffen wake, yau kusan shekaru uku kenan.
Title :
Al'ummar Garin Keffi Na Fama Da Rashin Ruwan Sha
Description : Daga Sani Musa Al'ummar keffi dake jihar Nassarawa sun koka dangane da matsalar ruwan sha dake suke fama da ita. Wasu daga cikin muta...
Rating :
5