Dubban 'yan Nijeriya da suka yi hijira zuwa wasu sassa na kasar Kamaru a shekarar 2014 sakamakon rikicin Boko Haram sun soma dawowa gidajen su, musamman na yankin Gamboru Ngala, amma saidai yawancin su sun dawo sun tarar da gidajen su a rushe.
A 'yan kwanaki uku da suka gabata, sama da 'yan gudun hijirar guda dubu sha biyar ne suka tsallako daga gadar ruwa mai nisan mita 300 daga iyakar kasar Kamaru da Nijeriya, sakamakon kiran da sojoji suka yi musu na cewa su dawo gida komai ya soma lafawa.
Bincike ya nuna cewa a kullum 'yan gudun hijirar suna ci gaba da dawowa gidajensu, kamar yadda wani mazaunin yankin ya bayyana.
Title :
Yan Gudun Hijira Na Ci Gaba Da Dawowa A Wasu Yankunan Jihar Borno
Description : Dubban 'yan Nijeriya da suka yi hijira zuwa wasu sassa na kasar Kamaru a shekarar 2014 sakamakon rikicin Boko Haram sun soma dawowa gid...
Rating :
5