Maigidan da tsohon shugaban 'yan sanda na kasa Mike Okiro yake haya a Abuja ya ba shi takarda domin ya bar masa gidansa.
Majiyarmu ta gano cewa mai gidan ya kudiri aniyar yin hakan ne bayan da tsohon shugaban 'yan sandan ya ki barin gidan bayan kudin hayar sa ya kare da kuma wa'adin watanni uku da aka ba shi don barin gidan.
Gidan yana kan titin Katsina Ala ne a gundumar Maitama, Abuja.
Sannan kuma ya karbi hayar gidan ne kan naira milyan takwas na tsawon shekara biyu.
Yanzu dai mai gidan na shirin maka Okiro a kotu domin ganin ya tattara komatsansa ya bar masa gidansa. Sannan kuma har zuwa yanzu dai tsohon shugaban 'yan sandan bai ce komai ba kan lamarin.
Title :
Tsohon Shugaban 'Yan Sanda Na Kasa, Mike Okiro Ya kasa biyan kudin haya.
Description : Maigidan da tsohon shugaban 'yan sanda na kasa Mike Okiro yake haya a Abuja ya ba shi takarda domin ya bar masa gidansa. Majiyarmu ta g...
Rating :
5