Takardar da ke tattare da bayanai kan kasafin kudi na 2016 da shugaban kasa Muhammasu Buhari ya mikawa majalisar tarayya a ranar 22 ga watan da ya gabata ya bace a tsakanin majalisar, kamar yadda majiyarmu ta PREMIUM TIMES ta rawaito a yau. Majalisar dattijai ta so yin zama ne kan takardar a yau Talata.
Amma sai shugaban Sanatocin Ali Ndume ya kidima membobin majalisar da wannan labarin bacewar takardun a yayin zaman sirri da suka yi.
Tuni dai aka nada Sanata Danjuma Goje a matsayin wanda zai jagoranci tawagar da za su lalubo takardun, inda za su yi hadaka da gwamnatin tarayya ta bangaren mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin majalisar tarayya, Sanata Ita Enang da kuma ma'aikatar tsare-tsare.
Title :
Takardun Da Aka Baiwa Majalisa Wanda Ke Kunshe Da Rahotannin Kasafin Kudi Na 2016 Ya Bace
Description : Takardar da ke tattare da bayanai kan kasafin kudi na 2016 da shugaban kasa Muhammasu Buhari ya mikawa majalisar tarayya a ranar 22 ga wata...
Rating :
5