Rahotanni daga kafar watsa labarai ta talabijin na CNN, tarawaito cewa dakarun sojojin Nijeriya sun sami bayanan sirri dake cewa an gano wani gida a karkashin kasa a dajin Sambiza. Wanda rahotannin sirri suka tabbatarwa da sojojin Nijeriya akwai 'yan kungiyar boko haram a ciki tare da manyan kayan fada.
Majiyar ta CNN ta kara da cewa tuni sojojin suka yi wa wurin kawanya tare da jiragen sama na yaki a inda suke ta shawagi a wurin hade da motocin sulke na yaki su ma sun tunkaro wurin.
Majiyar ta kara da cewa hakika wannan al'amari akwai nasara a cikin wannan dabarun yaki da sojojin suke yi a halin yanzu, skamakon yanzu sun gamsu da makaman da suke tunkarar mayakan kungiyar Boko Haram. Sabanin baya da ba su da makamai na kwarai ga kuma gazawar kwamandodi masu himma da kwazo. Don haka daga kowane lokaci a halin yanzu sojojin za su iya kawo karshen kungiyar Boko Haram a Nijeriya da kasashen da ke makwaftaka da ita wadanda su matsalar 'yan ta'addan ya shafa.
Title :
Sojoji Sun Kewaye Wani Gidan Kasa Da 'Yan Boko Haram Suka Fake A Dajin Sambisa
Description : Rahotanni daga kafar watsa labarai ta talabijin na CNN, tarawaito cewa dakarun sojojin Nijeriya sun sami bayanan sirri dake cewa an gano wa...
Rating :
5