An haifi Sir Abubakar Tafawa Balewa a garin Tafawa Balewa dake jihar Bauchi a Arewa maso Gabashin kasar nan, a shekarar 1912.
Ya kasance mutum mai da'a da kuma asali kasancewar mahaifinsa ma'aikaci ne ga hakimin garin.
Ya yi karatu a makarantar horon Malamai ta Katsina daga ( 1928 zuwa 1933), sannan ya zamo Malami, kuma shugaban makarantar 'Bauchi Middle School'.
Ya yi karatu a makarantar horas da malamai ta London daga 1945 zuwa 1946, inda ya samu shaidar malanta.
A lokacin yakin duniya na biyu ya nuna sha'awarsa ta shiga harkokin siyasa, inda ya kafa zauren tattaunawa na 'Bauchi Discussion Circle'.
Sannan daga bisani ya shiga siyasar Malamai, inda aka zabe shi mataimakin shugaban kungiyar Malaman Arewa.
A shekarar 1952 ya zamo ministan ayyuka na Nijeriya, ministan sufuri a 1954, sannan ya zamo jagoran jam'iyyar NPC a majalisar wakilai ta kasa.
Ya zamo Fira Ministan farko na Nijeriya bayan da kasar ta samu 'yancin kai a shekarar 1960.
A shekarar 1966, wasu sojoji suka yi kokarin juyin mulki, inda a nan ne aka sace shi kafin daga bisani aka kashe marigayi Sir Abubakar Tafawa Balewa.
Title :
Shekara 50 Bayan Rasuwar Tafawa Balewa: Ga Takaitaccen Tarihinsa
Description : An haifi Sir Abubakar Tafawa Balewa a garin Tafawa Balewa dake jihar Bauchi a Arewa maso Gabashin kasar nan, a shekarar 1912. Ya kasance m...
Rating :
5