Wata matashiya da ba a bayyana sunanta ba, an ceto ta daga cikin wani rami, inda ake zargin wani matsafin saurayinta ne ya ajiye ta a wurin.
Majiyarmu ta bayyana cewa lamarin ya auku ne a kasar Tanzania, inda ake zaton ta dauki kusan tsawon watanni takwas a ramin, kuma ana ciyar da ita ne sau biyu a mako.
Bayan an bankado ta daga ramin da aka boye ta, an yi gaggawar garzayawa da ita asibiti domin ba ta kyakkyawar kulawa.
Wata majiya ta bayyana cewa saurayin nata matsafi ne kuma ana zaton ya yi mata hakan ne bisa wasu dalilan su na matsafa.
Tuni dai jami'an tsaro suka cika hannu da shi, inda ake kan gudanar da bincike akan sa game da cin zarafin budurwar tasa da ya yi.
Title :
Saurayi Ya Garkame Budurwarsa A Rami Har Tsawon Watanni Takwas Domin Yin Tsafi Da Ita
Description : Wata matashiya da ba a bayyana sunanta ba, an ceto ta daga cikin wani rami, inda ake zargin wani matsafin saurayinta ne ya ajiye ta a wurin...
Rating :
5