Kasar Saudiyya ta bai wa ma'aikatan jakadancin Iran da ke kasar kwanaki biyu su fice daga kasar bayan ta yanke huldar jakadanci da ita sakamakon sabanin da kasashe biyun suka samu bayan zartar da hukuncin kisa a kan wani fitaccen Malamin Shi'a, Sheikh Nimr al-Nimr.
Ministan harkokin wajen Saudiyya Adil Al Jubair ya zargi Iran da kafa wasu gungun 'yan ta'adda tare da raba musu makamai a yankin.
Ya ce an ba wa jami'an jakadancin Iran kwanaki biyu su tattara nasu-ya-nasu su fice daga Saudiyya.
A ranar Asabar din da ta gabata ne masu zanga-zanga suka far ma ofishin jakadancin Saudiyya da ke Tehran, domin nuna fushinsu game da kisan da aka yi wa Sheikh Nimr al-Nimr da wasu mutum 46, wadanda aka ce an kama su da laifin ta'addanci.
Mahukunta a Iran dai na kallon Malamin a matsayin wanda ya yi shahada, wanda kuma ya goyi bayan zanga-zangar lumana.
BBC Hausa
Title :
Saudiyya ta kori ma'aikatan jakadancin Iran
Description : Kasar Saudiyya ta bai wa ma'aikatan jakadancin Iran da ke kasar kwanaki biyu su fice daga kasar bayan ta yanke huldar jakadanci da ita s...
Rating :
5