Hotunan Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi, A Yayin Da ya Je Kasar Sudan Domin Halartar Nikin Cika Shekaru 50 Da Kafa Jami'ar da Ya Yi Karatu
Sarkin yazo kasar Sudan ne domin halartar taron bikin cika shekara 50 da kafa jami'ar kasa da kasa ta (Africa International university of Africa).
Sarkin yana cikin daliban wannan jami'a, inda ya yi digiri a bangaran shari'a.
Daga cikin wadanda suka rufa wa Sarkin baya akwai Wamban Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, Dakta Bashir da Dakta Aliyu Haruna.
Daga cikin wadanda suka tarbe shi kuma a yayin isar sa kasar ta Sudan, akwai jakadan Nijeriya a kasar Sudan, Halluru Sodangi Shuaibu, shugaban jami'ar (I.U.A), Farfesa Kamalu Ubaid, Sarkin Fulanin Sudan, Sarkin Barebarin Sudan da sauran manyan mutane da dama.
Title :
Photos: Sarkin Kano Ya Ziyarci Sudan
Description : Hotunan Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi, A Yayin Da ya Je Kasar Sudan Domin Halartar Nikin Cika Shekaru 50 Da Kafa Jami'ar da ...
Rating :
5