Dan wasan kwallon kafar Borussia Dortmund da kasar Gabon Pierre-Emerick Aubameyang ne ya lashe kyautar lambar yabon gwarzon dan kwallon kafar Afrika na hukumar kula da kwallon kafar Afrika CAF na shekarar 2015.
Ya samu nasara ne a kan abokan takarar sa Yaya Toure na kulob din Manchester City da kasar Ivory Coast, wanda ya so ya lashe gasar a karo na biyar.
Andre Ayew na kasar Ghana ne ya zo na uku a takarar.
Dan kasar Tanzania Mbwana Aly Samatta ne ya lashe gwarzon dan kwallon Afrika da ke wasa a nahiyar Afrika.
Shi ne mutum na farko daga yankin gabashin Afrika da ya lashe kambun, wanda aka ware wa 'yan wasa da ke taka leda a kulob-kulob da ke nahiyar Afrika.
'Yar wasan kwallon kafa ta mata a Kamaru Gaelle Enganamouit ce ta lashe gwarzuwar 'yar kwallon kafa ta mata a nahiyar Afrika.
Najeriya mai masaukin baki ta samu nasarar lashe lambobin yabo biyu da suka hadar da Victor Osimhen wanda ya lashe gwarzon matshin dan wasan kwallon kafa na Afrika da kuma Etebo Peter Oghenekaro wanda ya lashe dan wasa da ke da baiwar kwallo da ake sa ran zai yi tashe nan gaba a nahiyar Afrika.
An dai gudanar da kade-kade da raye raye a dandalin taro na International Conference Centre da ke Abujan Najeriya inda aka gudanar da bikin bayar da kyautar.
Title :
Photos :Aubameyang Ne Gwarzon Kwallon Kafar Afrika
Description : Dan wasan kwallon kafar Borussia Dortmund da kasar Gabon Pierre-Emerick Aubameyang ne ya lashe kyautar lambar yabon gwarzon dan kwallon kafa...
Rating :
5