Babbar jam'iyya mai adawa ta PDP ta nemi majalisar kasa ta gaggauta tsige shugaba Buhari kan abun da suka kira babban abin kunya na bacewar kudin kasafin kudi.
Shugaban PDP Uche Secondus shi yayi wannan kira inda yace labaran da yake samu na cewa an samu kasafin kudi biyu, wanda hakan babban laifi ne da gwamnatin Buhari ta tafka.
Secondus ya baiwa 'yan Nijeriya hakurin halin matsi da suke ciki inda yace farashin dalar Amurka daya yau yakai Naira 305 a hannun gwamnatin da tayi tallan zata maida dalar Amurka daraja daya da Nairar Nijeriya.
Secondus yace wadannan laifuffuka da gwamnatin Buhari ta tafka tasa ko dai Buhari yayi murabus don radin kansa ko kuma majalisa ta gaggauta tsige shi domin tashin da Naira tayi shekaru 43 ba a ga irin haka ba. —
Title :
PDP Ta Nima A Tsige Buhari Akan Bacewar Takardun Kasafin Kudi
Description : Babbar jam'iyya mai adawa ta PDP ta nemi majalisar kasa ta gaggauta tsige shugaba Buhari kan abun da suka kira babban abin kunya na bac...
Rating :
5