Babban hafsan sojjojin kasa na Nijeriya, Liyutanal Janar Tukur Burutai ya ce rundunar sojin kasar za ta dauki sojoji 12,000 aiki a wannan shekarar.
Janar Burutai dai ya bayyana haka ne a wajen wata lacca mai taken "Sojin Najeriya: Kalubale da makomarsu" a kwalejin tsaro ta kasa da ke Abuja.
Ya kara da cewar za a kara yawan dakarun cikin shekaru takwas su zama su fiye da 200,000.
Babban hafsan sojin ya ce kuma hukumar sojin kasar za ta kafa wasu rundunoni biyu a arewaci da kudu maso kudancin kasar.
Sai dai bai fadi ainihin jihar da za a girke rundunar a yankin kudu maso kudancin kasar ba.
Janar Burutai ya ce kafa rundunonin biyu watau runduna ta takwas da kuma ta shida, wani bangare ne na wani muhimmin shirin da sojin ke yi domin bukasa ayyukansu a kan masu tayar da kayar baya, musamman a yankuna a zagayen tafkin Chadi.
Title :
Nijeriya Za Ta Dauki Karin Sojoji Dubu 12 Aiki
Description : Babban hafsan sojjojin kasa na Nijeriya, Liyutanal Janar Tukur Burutai ya ce rundunar sojin kasar za ta dauki sojoji 12,000 aiki a wannan s...
Rating :
5