Shugaban rundunar sojoji Laftanal Janar Tukur Buratai ya jinjinawa dakarunsa bisa murkushe 'yan ta'adda da suka yi a yankunan Arewa maso Gabas.
Buratai, wanda ya bayyana hakan a karshen makon nan a wurin bikin kaddamar da wani gini a cikin hedikwatar sojoji reshen garin Fatakwat, ya kara da cewa sojojin za su ci gaba da jajircewa don ganin sun kawar da duk wasu al'amuran ta'addanci a kasar nan.
"Yanzu mun yi nasara a kan 'yan ta'adda a yankunan Arewa maso Gabas, kuma hakan ba zai sa mu yin kasa a gwuiwa ba, za mu ci gaba da sanya ido", inji Buratai.
Title :
Mun Yi Nasara Kan Boko Haram - Janar Buratai
Description : Shugaban rundunar sojoji Laftanal Janar Tukur Buratai ya jinjinawa dakarunsa bisa murkushe 'yan ta'adda da suka yi a yankunan Arewa...
Rating :
5