DAGA IBRAHIM AMMANI, KADUNA
Gwamnonin jihohi bakwai wadanda suka yi iyaka da Kungurmin dajin Kamuku dake yankin karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna, sun bayyana cewar sun samu nasarar karya lagon barayin shanu wadanda suka addabi yankin.
Mai magana da yawun Gwamnonin, Aminu Bello Masari na jihar Katsina shi ya bayyana hakan ga manema labarai, jim kadan bayan kammala wani taron sirri da gwamnoni suka aiwatar na tsawon sa'o'i hudu a fadar gwamnatin jihar kaduna.
Gwamna Masari ya ci gaba da cewar sakamakon hadin gwiwar da sukayi na yaki da 'yan ta'adda a yankin, sunyi nasarar kwato Shanu har guda Dubu Talatin daga hannun barayin Shanun, wanda wannan ba karamar nasara bace inji shi.
Gwamnan na Katsina ya kara da cewar, ko shakka babu da akwai muggan 'yan fashi dake rayuwa a cikin kungurmin dajin Kamuku wanda suke addabar jama'ar yankunan da sukayi iyaka dasu, amma sakamakon matakan da gwamnonin yankin suka dauka, ya zamana yanzu komai yayi sauki.
Dangane da batun satar mutane dayin garkuwa dasu, da yanzu ake fama dasu a wasu yankunan jihohin Arewa kuwa, Aminu Masari yace hakan ya biyo bayan dakile satar shanun da sukayi ne, ya sanya Barayin sauya dabara, inda ya tabbatar da cewar zasuyi maganin su.
Gwamnonin jihohin Kaduna, Katsina, Kebbi, Kano, Naija, Sokoto da Zamfara, jihohin dake fama da wannan matsala ta ta satar shanu, dukkaninsu sun halarci wannan taron.
Title :
Mun Karya Laggon Barayin Shanu - Gwamnonin Arewa
Description : DAGA IBRAHIM AMMANI, KADUNA Gwamnonin jihohi bakwai wadanda suka yi iyaka da Kungurmin dajin Kamuku dake yankin karamar hukumar Birnin Gwa...
Rating :
5