Bayanan dake shigowa yanzu na cewa kotun kolin kasar nan ta amince da zaben jihar River wanda ya baiwa dan takarar PDP Nylso Wike nasara.
A baya dai kotun sauraren koke-koken zabe ta sauke zaben inda gwamna Wike ya tafi kotun daukaka kara don kalubalantar hukuncin wanda anan ya samu nasara. Wannan yasa dan takarar APC Dakuku Peterside shima ya tafi kotun koli don ganin abinda zai ture wa buzu nadi.
Alkalan kotun sun nemi da sai a watan gobe ne za a fitar da takardun sakamakon shari'ar ta yau.
Zaben na gwamna a jihar Rivers na cike da kura-kurai kamar yadda masu sanya ido a zabuka na cikin gida da na waje suka ce
Title :
KOTUN KOLI TA AMINCE DA ZABEN JIHAR RIVERS
Description : Bayanan dake shigowa yanzu na cewa kotun kolin kasar nan ta amince da zaben jihar River wanda ya baiwa dan takarar PDP Nylso Wike nasara. ...
Rating :
5