Babban kotun tarayya da ke zama a Maitama, Abuja, a yau Alhamis ta dage sauraren karar tsohon mai baiwa shigaban kasa shawara kan harkar tsaro Kanal Sambo Dasuki, sakamakon rashin halartar lauyoyinsa, Mista Joseoh Daudu da Mista Ahmed Raji, wadanda suka rubuta wasika ga kotun cewa sun halarci shari'a kan zabe a jihar Kogi a yau.
Hakan ya sa mai shari'a Baba Yusuf ya dage sauraren karar zuwa karfe 11 na safiyar gobe Juma'a.
Title :
Kotu Ta Dage Sauraren Shari'at Dasuki Sakamakon Rashin Halartar Lauyoyinsa
Description : Babban kotun tarayya da ke zama a Maitama, Abuja, a yau Alhamis ta dage sauraren karar tsohon mai baiwa shigaban kasa shawara kan harkar ts...
Rating :
5