A yau Talata ne aka kawo kakakin jam'iyyar PDP, Olisa Mutuh babbar kotun tarayya dake Abuja cikin ankwa.
Ana tuhumar Metuh ne da karbar naira milyan 400 na kudin sayen makamai domin yakar Boko Haram, daga wurin tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, Kanal Sambo Dasuki.
Daga baya dai kotun ta bada belin Metuh. Inda bayan sharrudan bada belin, kotu ta bukaci Metuh ya biya naira milyan 400.
Sannan kuna an bukaci ya gabatar da mutane biyu da za su tsaya masa, kuma kowannensu zai ba da naira milyan 200.
Ana kuma bukatar wadanda za su tsaya masa su kasance sun mallaki gida a yankin Maitama dake Abuja.
Title :
Kotu Ta Bada Belin Sakataren Jam'iyya PDP, Olisa Metuh
Description : A yau Talata ne aka kawo kakakin jam'iyyar PDP, Olisa Mutuh babbar kotun tarayya dake Abuja cikin ankwa. Ana tuhumar Metuh ne da karba...
Rating :
5