DAGA IBRAHIM AMMANI, KADUNA
Kisan wani matashi da wasu wadanda ake kyautata zaton cewa 'yan daba ne suka yi a harabar makarantar Capital da ke kan titin Rabah Kaduna, ya jefa dimbin jama'a cikin tarardadi da rudani.
Kamar yadda wani shaidar gani da ido mai suna Jibirila ya shaidawa RARIYA cewar, rikicin ya faru ne da safiyar Juma'a wajen karfe goma na safe, inda wasu matasa dauke da makamai, suka yi wa wannan matashi kofar rago, suka yi ta sarar sa babu ji babu gani, har sai da suka tabbatar ba ya motsi, sannan suka arce da gudu.
Lokacin da RARIYA ta isa wajen ta tarar da iyayen yara dake makarantar, suna ta jigilar 'ya'yansu suna mayar da su gida domin fargabar abin da zai iya faruwa biyo bayan wannan ta'addanci da aka yi.
Wasu jama'a da RARIYA ta zanta da su a wajen sun bayyana cewar, unguwannin Malali da Badarawa wadanda ke makwaftaka da makarantar da aka yi kisan, unguwanni ne da ke fama da matsalar matasa 'yan daba wadanda ba sa shakar kowa, kuma ana yawan samun karon batta a tsakanin su.
Kokarin RARIYA na jin ta bakin jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sanda dake jihar ASP Zubairu akan wannan lamari, ya ci tura saboda wayar sa tana ta kara ya ki dauka.
Title :
Kisan Wani Matashi A Garin Kaduna Ya Jefa Jama'a Cikin Dar-dar
Description : DAGA IBRAHIM AMMANI, KADUNA Kisan wani matashi da wasu wadanda ake kyautata zaton cewa 'yan daba ne suka yi a harabar makarantar Capit...
Rating :
5