A yayin karin haeke da hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa, NEMA ta yi game da bam din da ya tashi a garin Gombi da ke jihar Adamawa, ta bayyana cewa mutane takwas ne suka mutu a harin, wanda wasu 'yan kunar bakin wake suka kai a yau Juma'a.
Babban jami'in hukumar da ke kula da yankin Arewa maso Gabas, Alhaji Muhammad Kanar, ya shaida cewa mutane 28 suka ne jikkata a harin, wanda aka kai a wata kasuwa da ke garin na Gombi.
A cewarsa, cikin wadanda suka mutu har da 'yan kunar bakin waken guda biyu.
Ya kara da cewa tuni aka kai da wadanda suka jikkata asibiti domin kulawa da su.
Wani da yake wurin a lokacin da lamarin ya auku, ya bayyana cewa 'yan kunar bakin waken sun tayar da bama baman da ke jikinsu ne a lokacin da kasuwar ke cike da jama'a.
Title :
Kimanin Mutane Takwas Ne Bam Ya Halaka A Jihar Adamawa
Description : A yayin karin haeke da hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa, NEMA ta yi game da bam din da ya tashi a garin Gombi da ke jihar Adamawa, t...
Rating :
5