Yana zaune cikin motarsa ya zuro k'afa d'aya waje. Jafar ya zagaya ya shiga ciki ya zauna sukayi musabaha. Ganin fuskar Haris da alamun damuwa yace
"Lafiya na ganka wani iri kuwa?"
Haris ya sauke ajiyar zuciya
"Dole ai ka ganni haka,Ummina ce take neman rikitani da daren nan."
"Toh,menene ya faru?"
"Kishin fa? Akan tayi kirana har sau biyar ban amsa ba kuma sanin da tayi ina gidana ne ya sanyata zargi. Nayi rarrashin duniya tak'i saukowa. Bayan wannan kuma na kara laifi,kwana biyun da nayi gidan Rahma ayyuka sunmin yawa na kasa lekawa wajensu saidai waya kaga dole nayi laifi. Nidai yanzu taimakamin zakayi muje ka bata hakuri ko zata hakura na gaji da wannan horon rashin kulani da takeyi wallahi na damu sosai na gaza samun kwanciyar hankalina."
Jafar yace
"Shikenan,kayi jirana na chanja kaya."
"Kai haba,muje kawai mana."
Jafar ya harareshi yana kokarin bude motar
"Ta yaya zanje gaban suruka a haka? Nida zanyi sulhu saita rainani."
Sukayi dariya sannan Jafar ya koma ciki. Ya sanya dogon wandon jeans,ya chanja t-shirt sannan ya leka Siyama.
"Madam bari muje mu dawo."
Ta tsaida idanunta gareshi tana k'are mishi kallo. Yayi fes dashi sai kamshi yake. Zargi ya d'arsu a zuciyarta,kada dai zance Jafar zaije?
"Ina zakaje?"
Kallo d'aya ya yiwa kwayar idanunta ya hango matsanancin kishi,wani shu'umin murmushi yayi yana kasheta da kallonsa mai rikita gangar jikinta
"Wajen kanwarki zaimin rakiya,yanzu zamu dawo."
Da sauri ta nufoshi ai kuwa ya juya ya fita a guje yana dariya ya barta tana huci. Ta kasa zaune,wai meke faruwa ne? Ya Salam,no!!! Jafar bazai taba aure ba!!! Bai isa ba!!!!!! Bazai sanya Hajiya da yan uwana suyimin dariya ba!!!!! Har abada!!!!! Nawa ne ni kad'ai!! Babu wacce ya isa ya so!!!
****
"Yana sona,yana kaunata. Naga hakan a kwayar idanuwansa. Bazan barshi ba saidai zan bashi wahala kamar yanda ya wahalarmin da zuciyata. Saidai ina burin zama matar yaya j!!! Allah Ya azurtani da samunshi matsayin mijina!!!"
Cewar Ladi kenan a ranta,tana zaune ita d'aya a falonsu yayin data zubawa lambarsa ido wanda ta riga ta haddace a kwakwalwarta,tana kallo tana murmushi..
Dakyar Jafar ya lallaba Abida ta hanyar nasiha da ban baki har dai ta sauko sai gashi itace har da hira da dariya. Haris kamar ya shige jikinta tsabar jin dadi. Jafar kam wannan ba bakon abu bane a wajenshi,yasan soyayyarsu sosai don Haris bai kunyarsa. Ya mike tsaye yana duban agogon bangon
"Sha daya saura? Lallai na zaunu a gidan nan,nasan madam tana can a cike."
Haris ya mike tsaye yana dariya
"Ahaf,Allah Sarki madam,munyi mata laifi kam."
Jafar na dariya yace
"Don ma bakasan me nace mata bane."
Ya basu labarin yanda sukayi,dariya duk suka sanya har Ummi. Kafin Ummi tace
"Lallai ka b'allo ruwa Jafar. Kishi babu sauki."
Jafar yayi murmushi kawai ya dubi Haris
"Sai kazo ka mayar dani ko?"
Haris ya harareshi
"Gaskiya saidai na baka mukullin idan yaso da safe sai nazo na karb'a. Bazan iya fita ko'ina ba nabar Ummina."
Ai sai ran Ummi ya k'ara sanyi sosai,tayi wani murmushin jin dadi.
Hakan kuwa sukayi,ya rakashi har kofa. Anan ma Jafar ya dubeshi cike da damuwa
"Kasan Allah,nima na soma tunanin k'ara auren nan. Na gaji da halayyar Siyama."
Haris yace
"Wai har yanzu bata chanja zani bane?"
Ya tab'e baki kad'an yana mai numfasawa
"Ta ina fa? Abun ma sai k'ara gaba yakeyi Haris. Nikam na gaji,zan auro wacce ta iya tsafta da girki ko don na more rayuwar aure. Ko a wajen Allah bani da laifi,bayan da auren sama da d'aya ya zama halal,na bawa Siyama dama da yawa don ta gyara saidai hakan ko kadan bai samu ba duk hakurin da nakeyi da ita. Babu mai tsaidani gun k'ara auren nan saidai idan Allah Ya kaddaro bazanyi bane."
Haris cikin damuwa da tausayawa Jafar yace
"Gaskiyane,ni shaidane akan hakurin da kayi. Toh kana da wacce zaka aura ne?"
Jafar ya basar tamkar baiji ba yana mai kauda kansa gefe kafin ya juyo
"Wai ya ciwon k'afar Hajiyarmu ne? Na kwana biyu ban leka ba amma inason shiga wajen gobe. Ga babbar sallah baifi saura wata biyu ba."
Haris yayi dariya
"Hajiya sunje Jeddah a k'ara duba kafar watakila aiki za'ayi mata. Tare da Yaya Muttaka suka tafi. Baka bani amsar tambayata ba,wacece amaryar?"
Jafar ya hau sosa karan hancinsa yana murmushi kafin ya yamutse fuska
"Wai ma meye ruwanka? Kai malam nifa inada kishi ok? So,ka rabu da wannan maganar ma,bazan iya gwada maka ko wacece ba yanzu. Saida safe."
Ya fada motar yana kokarin tayarwa,Haris yana tuntsira dariya
"Dan iskan karya,idan tayi wari zanji ne. Gama kumbiya kumbiyarka..."
Jafar yana dariya yaja motar ya bar layin ba tare da ya bashi amsar komai ba.
Ya kalleta yaga tana faman huci ta cika tayi fam,yayi mugun murmushi
"Zaki bani hanya na shige ko kuwa dai anan zamu kwana?"
Ta kauce tayi ciki a zuciye,har lokacin bai bar murmushinsa ba. Bayan ya rufe kofar ya shiga ciki. Yana kokarin bud'e d'akin yaji muryarta
"Jafar baka isa ka k'ara aure ka kawo wata gidan nan ba wallahi. Har ni zakayiwa haka?"
Baice mata uffan ba har ya shige ya soma rage kayan jikinsa
"Ina magana kayi shiru? Nasan duk wannan zugar daga Haris take. Ganin da yayi ya k'ara aure shine yake neman ya doraka a hanyar daya bi ko? Toh wallahi ku sani,ni ba Ummi bace da kuka rainawa hankali ita kuma ta iya dauka! Dole ne ayau na shaida maka ni Siyama ni kadai ce mallakinka....."
"Ke wai baki da hankali ne? Kin cikamin dodon kunne,ga bacci inaji. Please get out?!!!"
Ya fada cikin daga murya don tun yana dariya har ta soma bashi haushi. Ta juya sumi sumi ta fice tana kunkuni,ashe dai dagaske yake auren yake nema. Lallai Jafar mugun butulu ne,duk yanda ta bijirewa zabin hajiyarta ta amince zata zauna dashi a halin da yake na wanda bai ajiye komai ba shine don tsabagen rainin hankali har yake da bakin ce mata yaje wajen kanwarta?
Daren kwanan bakin ciki Siyama tayi,batasan tana son mijinta ba sai yanzu.
******
Bayan sati daya da yin haka,dakyar tabar fushinta ta sauko da Jafar ya shaida mata wasa yakeyi.
Zuwa lokacin ya gama kaiwa kololuwar damuwana rashin ji da ganin Ladi. Gaba daya ta dauke kafarta daga shagon,gashi yana jin kunyar Mama bazai iya tambayarta komai game da Ladi ba.
Ladi kuwa duk da cewa tana zumudi da son yin tozali da yaya j,wannanbaisa ta amince ta kuma bayar da kanta ba. Tana sane take mishi hakan,taci sa'a lokacin suna kan rubuta exams,da wannan ta fake ta cewa Mama bazata samu damar zuwa shago ba har sai sun kammala.
*****
WATA RANAR ASABAR LADI TA DAUKI MATSANANCIN KWALLIYA.
Wata ranar alhamis Ladi ta dauki matsananciyar kwalliya cikin wani rantsetsan material kalar orange. Mai adon duwatsu,riga da siket ne sun zauna cif a jikinta. Ta tufke gashinta da manyan ribbons guda biyu ana hangensu ta cikin wadataccen mayafin data yafa a saman kanta. Hannunta rike da wayarta sai karamar jakarta data ratayo a kafad'a tana shirin sanya kanta cikin shagon sukayi kicibus dashi yana shirin fitowa.
Kamshin turarensa ya bugi hancinta da sauri taja baya ta d'ago tana dubansa. Ya ganta a rashin zato da tsammaninsa. Tuni ya fidda ran sanyata a idonsa a wannan ranar ma ganin ya kwashi fiye da mintuna talatin saboda son yaga sunyi arba.
Ya cigaba da bin fuskarta wacce tasha kwalliya da kallon da wa Allah Ya had'ani?
Ta sunkuyar da kanta tana murmushi ta russuna ta gaidashi kamar yanda ta saba. Ya k'i amsawa har tayi zaton kodai baiji ba,tunanin hakan yasa ta k'ara maimaitawa.
"Lafiya lau Deeya."
Ta mike sosai tana jiran ya bata hanya ta wuce, ya matsa gefe yana fadin
"Inason magana dake."
Gabanta yana faduwa ta karasa gefe nesa kadan dashi ta tsaya,ranta fari k'al har rawa takeyi gefeamma a fili sai ta nuna damuwa tana mai daure fuska. Batace komai ba,shi kuwa Jafar mamakinta yakeyi😮,wai daman Ladi ta iya fushi haka?
"Deeya wai har yanzu baki huce bane?"
Ta girgiza kanta,sai lokacin tayi wani Dan dan bazawarin murmushimai hade da fari
"Mekayi gareni yaya j da har zan rikeka?"
Ya kasheta da daya daga gwala gwalan murmushin(lol)
"Haba Deeya,ni nasan mai laifi ne. Toh idan ma kince bani da laifi meyasa kika haramtamin jin voice naki? Ko so kike na mutu? Please ki tausayawa mai kaunarki,ki bani lambarki kinji Deeya? Yaya j ne fa."
Ta rausayawar da kanta kafin ta dubeshi tayi murmushi,kamar bazata bashi ba sai kuma ta mik'a mishi hannu.
Ya dora wayarsa akan tafin hannunta na dama yana kasheta da kallon love,ta rubuta ta mika mishi.
Ya karba ya duba kafin ya saki murmushi karo na ba adadi ya sake kallonta
"Nagode deeya."
Daga haka ya fice, ta bi bayanshi da kallo tana murmushi hakoranta a bayyane.