Tsohon ministan yada labarai kuma gwamna a tsohuwar jihar Anmbara, Cif Jim Nwobodo a yau Juma'a ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa ta APC.
Nwobodo, wanda kuma tsohon sanata ne kuma tsohon dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDD, ya halarci taron APC da aka gudanar a jihar Enugu, wanda ya samu halartar ministan harkokin kasashen waje, Dakta Jeffery Onyeama.
Ya bayyana komawarsa jam'iyyar APC ne a wurin taron, wanda hakan ya baiwa membobin APC da dama da suka halarci taron mamki.
Title :
Jim Nwobodo Ya Bar PDP Zuwa APC
Description : Tsohon ministan yada labarai kuma gwamna a tsohuwar jihar Anmbara, Cif Jim Nwobodo a yau Juma'a ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP z...
Rating :
5