Jami'ar Jihar Kaduna (KASU) ta dakatar da wani malaminta mai suna John Dan Fulani a dalilin batanci da yake yi ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, Jam'iyyar APC, shugabnnin Arewa dabhar ma da mutanen yankin da suka marawa Buhari baya.
John Danfulani ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa manyan Arewa ne suka bata kasar nan, bayan batancin da ya yi ga mutanen yankin da shugaban kasa.
Sakamakon wadannan rubuce-rubucen ne ya sa aka dan samu zaman dar-dar a jihar saboda yinkurin da wadansu suka yi na afka wa John, cikinsu har da dalibai da suka fusata.
Jami'ar ta ce a matsayinsa na malamin dalibai bai kamata a ce irin wadannan kalamai na fitowa daga bakinsa ba wanda har ya kai ga na neman jawo rikici a jihar.
Title :
Jami'ar Kaduna Dakatar Da Wani Malaminta Kan Batanci Ga Buhari.
Description : Jami'ar Jihar Kaduna (KASU) ta dakatar da wani malaminta mai suna John Dan Fulani a dalilin batanci da yake yi ga shugaban kasa Muhamma...
Rating :
5