Rahotanni sun bayyana cewa Kanal Jafaru Lawal Isa ya maido da wasu kaso daga cikin kudin da ake zargin ya karba na kudin sayen makamai.
Jafaru wanda na hannun daman shugaban kasa Muhammadu Buhari ne a fannin siyasa, hukumar EFCC ta kama shi ne a ranar Larabar da ta gabata bayan an gano ya karbi wani kaso a kudin sayen makamai.
Bincike ya nuna cewa Jafaru, wanda shine memban jam'iyyar APC na farko da aka gano yana da hannu a badakalar kudin sayen makamai, ya dawo da milyan dari din ne a ranar Juma'ar da ta gabata ta wani akawun din bankin UBA.
Wani na hannun damansa ya bayyana cews Janar Jafaru, wanda tsohon gwamnan soja ne a jihar Kaduna kuma dan takarar gwamnan jihar Kano ne a karkashin jam'iyyar APC zaben 2011, ya nemi alfarmar dawo da ragowar naira milyan sittin nan ba da jimawa ba.
" Janar ya mayar da milyan dari ta akawun bankin UBA daga cikin milyan 160 da ya karba daga wurin Dasuki, wanda amini ne a wurinsa. Ba da jimawa ba kuma zai maido da ragowar milyan sittin.
"Ya dawo da kudin ne bayan an sanar da shi cewa kudin da Dasuki ya ba shi domin ya saya masa gida a Kano na sata ne", inda ya kara da cewa maigidan nasa bai san cewa kudin ba da guminsa Dasuki ya nema ba.
Ya ce a lokacin da aka bai shi kudin, bai san cewa na sata ba ne.
Title :
Jafaru Isa Ya Maido Da Milyan Dari Daga Cikin Kudin Da Dasuki Ya Ba Shi
Description : Rahotanni sun bayyana cewa Kanal Jafaru Lawal Isa ya maido da wasu kaso daga cikin kudin da ake zargin ya karba na kudin sayen makamai. Ja...
Rating :
5