*Ba Mu Mance Da Alkawuran Da Muka Daukarwa 'Yan Nijeriya Ba, Inji APC
"Kasancewa ta a fadar gwamnatin tarayya ba zai sanya na mance da wahalhalun da kuke sha ba, wadannan matsaloli da ake fuskanta na dan kankanin lokaci ne", kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyanawa al'ummar Nijeriya, wanda ke kunshe cikin sakon taya murnar shiga sabuwar shekarar 2016 da aika musu.
Shugaba Buhari ya kuma kara da cewa matsalolin da kasar nan ke fuskanta na wani dan kankanin lokaci ne domin za a shawo kansu nan bada jimawa ba.
Ya kuma tabbatar da cewa ba zai yi kasa a gwuiwa ba wajen cika wa al'ummar Nijeriya alkawuran da ya daukar musu.
A gefe daya kuma ita ma jam'iyyar APC ta jaddada cewa ba ta mance da alkawuran da ta daukarwa al'ummar Nijeriya ba, kamar yadda shugabanta John Odigie-Oyegun ya bayanna.
Title :
Ina Sane Da Wahalhalun Da Kuke Sha, Sakon Buhari Ga Al'ummar Nijeriya
Description : *Ba Mu Mance Da Alkawuran Da Muka Daukarwa 'Yan Nijeriya Ba, Inji APC "Kasancewa ta a fadar gwamnatin tarayya ba zai sanya na man...
Rating :
5