Daga Umar Bandi Kofar Kware
A matakin soma aiki da asusun bai daya, ga ma'aikatu gwamnatin jihar ta Sakkwato, wanda ya zama dalilin ta sami nasarar gano wasu makuddan kudade har Naira biliyan daya da dubu dari biyar a cikin asusunan kudi guda dari a bankunan kasar nan.
Kwamishinan kudin jihar Alhaji Umar Sa'idu ne ya bayyana haka a ranar lahadin da ta gabata, lokacin da yake bayani akan tsarin wanda gwamnati ta soma aiki da shi, kwamishinan yace tun lokacin da gwamnati ta soma amfani da wannan tsarin asusun bai daya, aka samu ci gaba, so sai a wajen sha'anin kudaden gwamnati, a tsakanin ita kanta gwamnati da bankuna da take amfani da su, ya kara da cewa wannan matakin ya taimaka a wajen rage kura kurran da ake samu, kuma ya kara inganta sha'anin kudi daga asusun.
Haka kuma ya yaba da amfani da wannan tsarin na asusun bai daya, ya kara da cewa ana nan ana kara inganta abubuwan da suka shafi kudi.
Title :
Gwamnatin Jihar Sokoto Ta Gano Wasu Kudi Fiye Da Naira Bilyan Daya Da Rabi
Description : Daga Umar Bandi Kofar Kware A matakin soma aiki da asusun bai daya, ga ma'aikatu gwamnatin jihar ta Sakkwato, wanda ya zama dalilin ta...
Rating :
5