DAGA IBRAHIM AMMANI, KADUNA
Gwamnatin jihar Kaduna karkashin Nasiru El Rufa'i ta kafa kwamitin bincike, wanda zai binciki dalilin faruwar rikicin daya afku a ranakun 12 da 14 na watan Disambar bara a tsakanin sojojin Nijeriya da 'yan Shi'ah a Zariya.
Kwamitin binciken na karkashin kundin tsarin bincike sashi na biyu na gwamnatin jihar kaduna, na shekarar 1991, kuma ana saran kwamitin zaiyi zama na makwanni shidda ya kammala bincikensa.
Membobin kwamitin sun tara manya Lauyoyi a ciki, Malamam addini, masu rajin kare hakkin dan Adam, masana tarihi da sauransu.
Mai shari'a Lawal Garba shine shugaban wannan kwamiti, wanda gabanin wannan matsayi shine shugaba na babbar kotun tarayya dake Fatakwal. Sai Farfesa Salihu Shehu wanda yake malami ne a jami'ar Bayero dake Kano. Sannan da akwai Farfesa Umar Labdo wanda Shehin malami ne a jami'ar Arewa maso yamma dake Kano. Sannan da akwai Malam Salihu Abubakar wanda ke sashin bincike akan ayyukan gona na jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya.
Sauran sun hada da Farfesa Auwalu Yadudu masanin shari'ah kuma tsohon mai baiwa marigayi tsohon shugaban kasa Abacha shawara akan harkokin shari'ah. Sai kuma Farfesa Ibrahim Gambari wanda tsohon Ministan harkokin waje ne, wanda yayi aiki a ofishin babban Sakataren majalisar dinkin duniya. Kwamitin zai fara zamane a makon gobe idan Allah ya kaimu.
Indai jama'a ba su mance ba, a wani jawabi da gwamna El Rufa'i ya yi kai tsaye, kuma aka watsa shi a kafafen yada labarai a kwanakin baya, ya yi alkawarin kafa kwamiti, wanda zai binciki dalilin wannan dauki ba dadi, wacce ta faru a tsakanin sojin Nijeriya da zugar 'yan Shi'a, lamarin da ya yi sanadiyar rasa rayuka masu yawa.
Title :
Gwamnatin El-Rufa'i Ta Kafa Kwamitin Bincike Akan Tarzomar 'Yan Shi'a Da Sojoji
Description : DAGA IBRAHIM AMMANI, KADUNA Gwamnatin jihar Kaduna karkashin Nasiru El Rufa'i ta kafa kwamitin bincike, wanda zai binciki dalilin faru...
Rating :
5