Daga Isyaka Laminu
Gwamnatin Jihar Bauchi karkaahin jagorancin Muhammad Abdullahi Abubakar ta rabawa matasa sabbin wayoyin hannun domin su rika kare martabarta a idon duniya, musamman kafafen yada labarai na zamani.
Mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Muhammad Abdullahi Abubakar kan yada labarai, Alhaji Kabiru Nuru Lemi shine ya raba wa matasa.
Da yake jawabi yayin rabon ya bukaci matasan da su yi iya kokarin su wajen kare manufofi da kuma wayar da kan Al'umma akan ayyukan gwamnatin jihar Bauchi.
Ya kara da cewa ba za su zuba ido yan adawa suna Amfani da kofofin yada labarai na zamani don cin mutuncin gwamnati da bata suna ba.
Daya daga cikin Matasan da suka samu kyautar wayar ta Ipad Ibrahim Dawaki Abubakar ya ce "Yau mai tallafa wa gwamna na musamman kan harkokin watsa labarai, Alh. Kabiru Lemi yaraba wa wasu yan' social media Ipads phone kiran Galaxy cikinsu hardani Ibrahim Dawaki Allah ya sakawa S.A Media".
Sai dai masu adawa da gwammatin na matakin a matsayin wani da zai iya kashe wa matasa zuciya.
Source Zumatimes
Title :
Gwamnatin Bauchi Ta Raba Wa Matasa Wayoyin Hannu Don Su Kare Muradunta
Description : Daga Isyaka Laminu Gwamnatin Jihar Bauchi karkaahin jagorancin Muhammad Abdullahi Abubakar ta rabawa matasa sabbin wayoyin hannun domin su...
Rating :
5