DAGA IBRAHIM AMMANI, KADUNA
Mutum biyu ne aka tabbatar da cewar sun kone kurmus, yayin da shaguna 700 suka cinye tatas, sakamakon afkuwar wata mahaukaciyar gobara data afku da talaitanin daren jiya Litinin har ya zuwa wayewar garin yau Talata a babbar kasuwar tashar jirgin kasa dake kaduna.
Da yake bayyana abinda ya ganewa idanuwanshi, wani mai gadi a kasuwar mai suna Malam Muhammadu Baba, yace gobarar ta samo asaline daga cikin wani shagon saida kaya na wasu Inyamurai, biyo bayan hasa wuta da sukeyi a cikin shagon da niyyar jin dumi, inda barci ya kwashe su sannan wuta ta kama shagon, bayan kankanin lokaci ta fantsama sauran shaguna.
Mai gadin ya cigaba da cewar nan take suka kira lambar wayar jami'an 'yan kwana-kwana amma wayar tayi ta kara basu dauka ba, dalilin daya sanya gobarar tayi munmunan ta'adi kenan.
Malam Abubakar Zakari shine jami'in hulda da jama'a na hukumar bada agajin gaggawa ta jihar kaduna SEMA, ya bayyana cewar tuni jami'an hukumar tasu suka isa wajen, domin ganewa idanuwansu abinda ke faruwa, sannan ya tabbatar da cewar hukumarsu zatayi dukkanin mai yiyuwa wajen tallafawa wadanda bala'in ya shafa.
Tuni dai gwamna Nasiru Ahmed El-Rufa'i ya ziyarci kasuwar, inda ya jajantawa 'yan kasuwar dangane da wannan bala'i daya afka musu, tare da alkawarin samun taimakon gwamnatin jihar.
Title :
Gobara Ta Hallaka Mutum Biyu Da Lalata Shaguna 700 A Kasuwar Railway Kaduna
Description : DAGA IBRAHIM AMMANI, KADUNA Mutum biyu ne aka tabbatar da cewar sun kone kurmus, yayin da shaguna 700 suka cinye tatas, sakamakon afkuwar ...
Rating :
5