SABUWAR BADAKALAR KUDIN SAYEN MAKAMAI
Gobe EFCC Za Ta Soma Gudanar Da Bincike Kan Wasu Manyan Hafsoshin Sojoji Guda 18
A gobe Litinin ne hukumar EFCC za ta soma gudanar da bincike kan wasu manyan hafsoahin sojoji guda sha takwas da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin a bincike su.
Majiyarmu ta Punch ta rawaito cewa tuni hukumar ta aikawa da wasu daga cikin janarorin sojojin da wasu kamfanonin da lamarin ya shafa, wadanda sunayen su ya fito cikin rahoton da aka gabatarwa da shugaban kasa takardar gayyata.
Wata majiya daga hukumar ta bayyana cewa "mun aika wasika ga yawancin su kuma daga nan zuwa gobe Litinin za su soma amsa gayyatar".
Idan ba a mance ba dai shugaba Buhari, a ranar Juma'ar da ta gabata ga umarci hukumar EFCC da ta fadada bincikenta bisa zargin wasu manyan hafsoshin sojojin kasa da na sama da wawushe bolyoyin kudade na sayen makamai.
Wadanda lamarin ya shafa sun hada da tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, Kanal Sambo Dasuki (mai ritaya); tsohon shugaban hafsan sojoji, Alex Badeh (mai ritaya); da kuma tsoffin shugabannin sojojin sama guda biyu, Air Marshal MD Umar (mai ritaya) da Air Marshal Adesola Amosun (mai ritaya).
Saura sun hada da Mejo Janar E.R Chioba (retd) AVM I.A Balogun (retd.); AVM A.G Tsakr (retd.); AVM A.G Idowu (retd.);AVM A.M Mamu; AVM O.T Oguntoyinbo; AVM T. Omenyi; AVM J.B Adigun; AVM R.A Ojuawo; AVM J.A Kayode-Beckley; Air Cdre SA Yushau (retd.); Air Cdre A.O Ogunjobi; Air Cdre G.M.D Gwani; Air Cdre S.O Makinde; Air Cdre A.Y Lassa; da Kanal N Ashinze.
Sai kuma sunayen kamfanonin da abin ya shafa sun hada Messrs Societe D’ Equipment Internationaux; Himma Aboubakar; Aeronautical Engineering and Technical Services Limited; Messrs Syrius Technologies; Dr. Theresa A. Ittu; Sky Experts Nig Ltd.; Omenyi Ifeanyi Tony; Huzee Nig. Ltd.; GAT Techno Dynamics Ltd.; Gbujie Peter Obie and Onuri Samuel Ugochukwu.
Sauran sun hada da Spacewebs Interservices Ltd.; Oguntoyinbo Tayo; Oguntoyinbo Funmi; Delfina Oil and Gas Ltd.; Chief Jacobs Bola; Mono Marine Corporation Nig. Ltd.; Geonel Intergrated Services Ltd.; Sachi Felicia; Mudaki Polycarp da Wolfgang Reinl.
Title :
EFCC Za Ta Soma Gudanar Da Bincike Kan Wasu Manyan Hafsoshin Sojoji Guda 18
Description : SABUWAR BADAKALAR KUDIN SAYEN MAKAMAI Gobe EFCC Za Ta Soma Gudanar Da Bincike Kan Wasu Manyan Hafsoshin Sojoji Guda 18 A gobe Litinin ne h...
Rating :
5