*****
Rahotannin dake shugo mana na cewa hukumar yaki da rashawa ta EFCC tayi awon gaba da wani jigo kuma makusanci ga janar Buhari a jihar Kano.
Lawan Jafaru Isa tsohon gwamnan jihar Kaduna ne lokacin marigayi janar Abacha, ya kuma yi takarar gwamnan Kano a tsohuwar jamiyyar CPC ta Buhari a zaben 2011, kuma yi sake takara a APC 2015 inda Ganduje ya kayar dashi a zaben fidda gwani.
A baya dai ana ta hasashen shi Jafaru Isa ne Buhari zai baiwa Mukamin minista daga Kano, kuma ko da aka gama raba mukaman ministoci bai samu ba anyi masa tsammanin babban rabo daga gwamnatin Buhari ganin yadda ya dade yana yada manufofin tafiyar Buhari a jihar Kano da kasa baki daya.
Rahotanni na cewa kamun da aka yiwa Jafaru Isa nada nasaba da kudin tsaro da akwa wawashe daga ofishin tsohon mashawarcin tsaro Sambo Dasuki, kuma ance tsohon gwamnan Sojan a ofishin hukamar ta EFCC a Abuja ya share daren jiya.
Title :
EFCC Tayi Awon Gaba Da Birigediya Jafaaru Isah
Description : ***** Rahotannin dake shugo mana na cewa hukumar yaki da rashawa ta EFCC tayi awon gaba da wani jigo kuma makusanci ga janar Buhari a jiha...
Rating :
5