EFCC Ta Yi Awon Gaba Da Daraktan Hukumar Kula Da Kafafofin Watsa Labarai Ta Kasa
Hukumar EFCC ta yi awon gaba da daraktan hukumar kula da kafafofin watsa labarai ta kasa (NBC), Emeka Mba bisa zargin salwantar naira bilyan 15.
Majiyarmu ta rawaito cewa an kama daraktan ne a safiyar yau Litinin a babban birnin tarayya Abuja, inda aka tallafa keyarsa zuwa hedikwatar hukumar domin amsa tambayoyi.
Majiyar ta mu ta kara da cewa hukumar ta soma tuhumar saraktan ne tun a watan da ya gabata. Sannan kuma a makon da ya gabata wasu daga cikin jami'an sun je hedikwatar ta NBC, inda suka kwashi kwamfutoci da takardu a sashen kudi. Haka kuma an yi awon gaba da wasu ma'aikatan sashen kudi na hukumar.
Title :
EFCC Ta Kama Shugaban NCC Emeka Mba
Description : EFCC Ta Yi Awon Gaba Da Daraktan Hukumar Kula Da Kafafofin Watsa Labarai Ta Kasa Hukumar EFCC ta yi awon gaba da daraktan hukumar kula da k...
Rating :
5