Wani rahoto da hukumar EFCC ta fitar na cewa hukumar ta gano wasu makudan kudade fiye da Naira tiriliyan a asusun wasu shugabanni tsaro da suka yi aiki a gwamnatocin baya.
Hukumar tace tuni ta dauki aniyar kiran wadannan tsaffin jami'ai don bincikar yadda aka samu wadannan makudan kudi a asusun ajiyarsu ta banki. Hukumar ta EFCC tayi karin hasken cewa ta gano wadannan kudade a wasu bankuna guda 4.
Ko a wancan sati hukumar ta cafke wani babban hafsan soja tare da wani Bajamusan bature kan almundahana da wasu kudade da aka fitar don horar da sojoji a kasar Bilarus amma kudaden suka yi layar zana.
Title :
EFCC Ta Gano Fiye Da Naira Tiriliyan A Asusun Wasu Tsaffin Shugabannin Sojojin
Description : Wani rahoto da hukumar EFCC ta fitar na cewa hukumar ta gano wasu makudan kudade fiye da Naira tiriliyan a asusun wasu shugabanni tsaro da ...
Rating :
5