*Yayin Da Har An Kamo Dansa
Hukumar EFCC ta kafa tawagar da za su kamo tsohon shugaban hafsan tsaro Alex Badeh da sauran wasu mutane 17 cikin har da manyan hafsoshin sojoji guda 11.
Hafsoshin sojojin dai, bincike ya nuna cewa suna da alaka da dala bilyan 2.1 na kudin sayen makamai.
Bincike ya nuna cewa sai kwamitin ta gudanar da bincike kan wasu daga cikin hafsoshin sojojin ne kafin daga bisani a mika su ga hukumar ta EFCC.
Daga cikin hafsoshin sojojin da za a tuhuma akwai tsoffin shugabannin sojojin sama guda biyu, Air Marshal M.D. Umar da A.N. Amosu(rtd).
Sai kuma wasu kamfanoni guda 22 da su ma za a tuhuma bisa zargin su da karbar wasu kaso na kudin makaman.
Sauran sun hada da manyan hafsoshin sojojin da za a tuhuma sun hada da: AVM A. M. Mamu; AVM O.T.Oguntoyinbo, AVM R.A. Ojuawo; AVM J.B. Adigun, AVM T Omenyi, Air Cdre A.O. Ogunjobi; Air Cdre G.M.D Gwani; Air Cdre S.O. Makinde; Air Cdre A.Y. Lassa da Col. N. Ashinze , wanda shine mataimaki na musamman ga tsohon mai baiwa shugaba kasa shawara kan harkar tsaro Kanal Sambo Dasuki.
A gefe daya kuma, rahotanni sun bayyana cewa tuni hukumar ta cafke dan gidan tsohon shugaban sojojin, Kanal Ashinze bisa zarginsa da hannu a badakalar kudin sayen makaman.
Title :
EFCC Na Shirin Kamo Badeh Da Sauransu
Description : *Yayin Da Har An Kamo Dansa Hukumar EFCC ta kafa tawagar da za su kamo tsohon shugaban hafsan tsaro Alex Badeh da sauran wasu mutane 17 ci...
Rating :
5