Jarumar fina-finan Hausar nan da ke fitowa a matsayin muguwa, Hajiya Saratu Gidado da aka fi sani da Daso ta ce daga yanzu ta daina hargagi a fina-finai kamar yadda take yi a da.
Daso ta ce ko da za ta fito a muguwa, to za ta dinga yin muguntar ne cikin natsuwa, ba kamar yadda ta saba fitowa ba.
Daso ta ce a zahiri ita ba muguwa ba ce
A hirar da BBC ta yi da jarumar ta shaida cewa tana fitowa a matsayin muguwa ne kawai saboda rawar da daraktocin fim ke son ta rika takawa ke nan, tana mai cewa a zahiri mugunta ba halinta ba ne.
TALLA
Daso ta ce, "Duk rawar da aka ce na taka zan iya yi, amma ba zan taka rawar da za a ce na kashe wani ba. A da ina yin hargowa ne saboda akwai kuruciya a jikina, amma yanzu shekaru sun tafi, ba zan iya zurawa da gudu ko in rika haragiyar fada kamar karya ba. Yanzu zan rika yin fim da 'class'. Zan fito a matsayin uwa ta gari ko kwamishina ko shugabar makaranta".
Saratu Daso, wacce ta fara fim a shekarar 2000, ta ce tana yin fim ne domin fadakarwa shi ya sa take fitowa a duk rawar da aka ce ta taka.
Title :
Daso Na Daina Fitowa A Matsayin Muguwa Saidai A Fim Mai Aji, Saratu Gidado Daso
Description : Jarumar fina-finan Hausar nan da ke fitowa a matsayin muguwa, Hajiya Saratu Gidado da aka fi sani da Daso ta ce daga yanzu ta daina hargagi...
Rating :
5