Yayin Da Aka Gano Wata 'Yar Shekara Takwas Dauke Da Cutar
Wata yarinya 'yar shekara takwas daga kauyen Lamban a karkashin karamar hukumar Yamaltu Deba dake jihar Gombe, an gano cewa tana dauke da cutar zazzabin lassa, kamar yadda daraktan lafiya na jihar, Dakta Joshua Abubakar ya bayyana a jiya.
Daraktan lafiyar ya bayyanawa manema labarai cewa an aika da samfurin yanayin halin da yarinyar take ciki ne zuwa dakin bincike a jihar Lagos, inda aka tabbatar da cewa tana dauke da cutar, inda ya kara da cewa yanzu haka an kebe ta wuri guda domin ba ta kulawa ta musamman a asibiti.
Ya kuma kara da cewa sun tura tawagarsu zuwa ga 'yan uwan yarinyar domin gano musabbabin abin da ya haddasa mata kamuwa da cutar. Sannan kuma ya kara da cewa akwai kusan mutane bakwai da aka kawo asibiti wadanda ake zargin sun kamu da cutar, amma daga bisani bincike da aka yi wa biyar daga cikin su ya nuna cewa basu dauke da cutar. Ya kuma shawarci jama'a da su kasance masu tsaftace muhallin su don
Title :
Cutar Zazzabin Lassa Ta Shigo Jihar Gombe,
Description : Yayin Da Aka Gano Wata 'Yar Shekara Takwas Dauke Da Cutar Wata yarinya 'yar shekara takwas daga kauyen Lamban a karkashin karamar ...
Rating :
5