Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kudiri aniyar dakatar da shirin da majalisar tarayya ke yi na sayen motoci har na kimanin naira bilyan 50 a jimlace, a daidai lokacin da kasar take fama da matsalar tattalin arziki.
Buhari ya kalubalanci kudirin ne a ranar Larabar da ta gabata a lokacin da yake hira da 'yan jaridu, inda ya ce shi kansa ya ki amincewa da kudirin saya masa motoci a kasafin 2016.
"Na yi watsi da kudirin saya min motoci har na kimanin naira milyan 400, saboda motocin da nake amfani da su suna da kyawun da za a kai shekaru goma masu zuwa ana amfani da su", inji Buhari.
Ya kuma kara da cewa yana fuskantar kalubale daga majalisar tarayyar kasancewar sun ki amincewa da tsarin asusun bai daya, kuma ga shi yanzu suna shirin sayen sabbin motoci.
A yayin tunatar da shi a natsayinsa na shugaban kasa, ko yana da ikon dakatar da kudirin sayen motocin, Buhari ya kara da cewa "zan yi amfani da iko na wajen hana sayawa majalisar tarayya motoci na kimanin naira bilyan hamsin".
"Idan har zan yi watsi da kudirin sayawa gwamnatin tarayya motoci na naira milyan 400 saboda matsalar tattalin arzikin da kasar ke fama da shi, ba zan sanya ido na ga majalisar tarayya ta sayi motoci na sama da naira bilyan 47 ba, duk da cewa ana biyan su alawus din zirga-zirga", kamar yadda shugaba Buhari ya kara da cewa.
Title :
Buhari Na Shirin Hana Sanatoci Da 'Yan Majalisu Sayen Motoci Na Kimanin Naira Bilyan 50
Description : Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kudiri aniyar dakatar da shirin da majalisar tarayya ke yi na sayen motoci har na kimanin naira bilyan 50...
Rating :
5