A jihar Borno arewacin Najeriya
rahotanni sun ce wasu yan bindiga da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun
kai hari garin Dalori da ke wajen birnin Maiduguri .
Rahotanin sun ce maharan sun kona gidaje da dama kuma an samu asarar rayuka.
Wani mazaunin garin da yanzu suke samun mafaka a cikin daji ya yiwa BBC karin bayani cewa an hallaka 'yan uwansa guda biyu.
Ya
ce maharan kai wa garin na Dalori mai nisan kilomita shida daga
Maiduguri babban birnin jihar farmaki da manyan bindigogi suka rika
harbin kan mai uwa da wabi.
Gwamnatin Najeriyar wacce ta lashi takobin murkushe 'yan kungiyar Boko Haram din na ikirarin cewa ta karya lagon mayakan
Title :
Boko Haram Ta Kai Hari Garin Dalori Dake Maiduguri
Description : A jihar Borno arewacin Najeriya rahotanni sun ce wasu yan bindiga da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun kai hari garin Dalori da ke...
Rating :
5